Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiCin zarafin Naira na haddasa wahala wajen buga sabbin takardun kudi a...

Cin zarafin Naira na haddasa wahala wajen buga sabbin takardun kudi a Najeriya – CBN

Babban bankin Najeriya CBN ya yi gargaɗin cewa cin zarafin Naira da wasu ke yi ne ke haddasa tsada da karin wahalhalu wajen buga sabbin takardun kudin da kuma maye gurbin su a bankuna.

Mataimakin shugaban sashen gudanar da ayyuka na bankin, Dr. Bala Bello, wanda ya samu wakilci ne ya bayyana hakan, a wajen bude gangamin wayar da kai kan yadda za a rika tu’ammali da takardar Naira a Abuja.

Ya ce muddin ba a dauki matakin magance wannan dabi’a ba, ‘yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar kalubale, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata