Hukumar da ke lura da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya NCDC ta ce mutum 167, ne suka rasu sakamakon kamuwa da cutar Lassa a Nijeriya, duk da raguwar sabbin masu kamuwa da ake samu.
A rahoton mako na 13 (23–29 Maris 2026), an samu sabbin kamuwa guda 26, ƙasa da 51 na makon da ya gabata.
Bayanan alkaluman rashe-rashen da hukumar ta tattaro ya kai 25.2 bisa 100, sama da 18.5 bisa 100 a shekarar 2025.
Jaridar Premium Times ta ambato an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar a jihohi bakwai kamar: Edo, Bauchi, Ondo, Taraba, Ebonyi, Benue da Kaduna, yayin da jihohi 22 suka samu aƙalla mutum ɗaya da ya kamu a bana.
Matasan da ke tsakanin shekaru 21 zuwa 30 su ne suka fi kamuwa, kuma babu sabon kamuwa a ma’aikatan lafiya a makon.
Hukumar ta ce tana ƙara matakan yaƙi da cutar tare da haɗin gwiwar hukumar da ke yaki da yaduwar cutuka ta duniya.
Ta kuma bayyana ƙalubale kamar jinkirin zuwa asibiti, tsadar magani, da rashin tsaftar muhalli a matsayin musabbabin dawowarta.
