Ministan yada labarai da wayar da kai na Nijeriya, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa na cikin muradun ceto tattalin arzikin kasa da amfanin daukacin ‘yan Najeriya.
Da yake karbar bakuncin kungiyar ‘yan jarida ta NGE a Abuja, Idris ya ce cire tallafin man fetur ya baiwa gwamnatocin jihohi damar samun karin kudaden shiga don yi wa jama’a ayyukan ci gaba.
Game da rancen dalibai, ya ce fiye da matasa 300,000 sun koma makaranta saboda gwamnatin tarayya na biyansu kudin makaranta da na rayuwa, inda aka kashe fiye da Naira biliyan 50 kan shirin.
A bangaren noma, ya bayyana cewa gwamnatin na ci gaba da kokari tare da kafa Ma’aikatar Kiwo ta farko a tarihin Najeriya, da kuma Ma’aikatar Harkokin Teku da Tattalin Arzikin Ruwa domin bunkasa arzikin kasa.
Rahoton jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Ahmed Idris na jaddada cigaban da Gwamnatin Tinubu ta samu kan tsaro, inda ya ce an samu ci gaba matuka idan aka kwatanta da shekarun baya, musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
