Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaDa na koma jam’iyyar APC a halin da Nijeriya ke ciki gara...

Da na koma jam’iyyar APC a halin da Nijeriya ke ciki gara na bar siyasa – Jigon ADC a Katsina

Fitaccen dan siyasa, jigo a jamiyyar hadaka ta ADC a Jihar Katsina, kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar ya fadi hakan ne a wata tattaunawar sa da DCL Hausa kwanaki kadan bayan sun kaddamar da jam’iyyar ADC a jihar

Jam’iyyun APC, PDP da NNPP a jihar sun gamu da babban koma baya, bayan dubban jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyun suka sauya sheka zuwa sabuwar hadakar ta ADC.

Daga cikin jiga-jigan PDP da suka koma ADC akwai tsohon sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Muhammad Inuwa da tsohon ministan tsaro a Nijeriya Lawal Batagarawa da tsohon sanata a shiyyar Daura Ahmed Babba Kaita da kuma Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da sauran su.

Tsohon sakataren ya ce sabon taken jam’iyyar ADC a Katsina “Nijeriya kowa yana ji a jikin shi, Katsina kuma akwai korafi.

muhammad kabir
muhammad kabirhttps://dclhausa.com
Muhammad Kabir, ƙwararren ɗan jarida ne wanda ke da gogewa a fannin yada labarai na zamani (Digital Media)...
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata