DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiDa ni ne shugaban kasa da na tafiyar da tattalin arziki fiye...

Da ni ne shugaban kasa da na tafiyar da tattalin arziki fiye da Tinubu – Peter Obi

Dan takarar jam’iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa a shekarar 2023 Peter Obi, ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki masu amfani.
Obi, wanda ya bayyana hakan a wata hira da yayi da Arise News, ya soki matakin shugaba Tinubu ya dauka na barin naira tana tangal-tangal a kasuwar canjin kudade, da kuma kara ciyo basussukan ga kasar da sauran matsalolin tattalin arziki. 
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya tabbatar da cewa, da a ce shi ne shugaban kasa, da kasar ta ga sauye-sauye masu inganci a cikin shekaru biyu fiye da Shugaba Tinubu.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata