Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiDaga cikin rarar tallafin man fetur za a yi wa filin jirgin...

Daga cikin rarar tallafin man fetur za a yi wa filin jirgin saman Lagos gyaran Naira biliyan 712 – Festus Keyamo

Ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya Festus Keyamo, ya kare shirin gwamnatin tarayya na sake fasalta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos da kudin na suka kai Naira biliyan 712, yana mai cewa hakan na da nufin yin gogayya da sauran filayen na duniya.

Yayin wata hira da tashar Channels Television a shirin Sunday Politics, Keyamo, wanda lauya ne mai matsayin SAN, ya bayyana cewa filin jirgin da aka gina sama da shekaru arba’in da suka wuce ya lalace matuka.

“Rufin tashar jirgin na yayyafa ruwa; wajen ya lalace kuma yana wari. Ana siyar da Indomie da wasu kayayyaki a ciki. Fankoki da ke tura kaya sun daina aiki saboda babu gyara,” in ji shi.

A makon da ya gabata, gwamnatin tarayya ta amince da kashe biliyan ₦712 don yin aikin, wanda hakan ya jawo cece-kuce daga jama’a da dama.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata