Sojojin Najeriya sun dakile hare-hare biyu da Boko Haram/ISWAP suka kai a daren Alhamis a Gajibo da Damboa, Jihar Borno.
Majiyoyi sun tabbatarwa Premiumtimes cewa maharan sun farmaki Gajibo da misalin karfe 11:30 na dare, amma sojoji sun fatattake su tare da samun karin dauki daga Dikwa. Inda aka hallaka daya daga cikin maharan, yayin da kuma wasu da dama suka tsere da raunuka.
Sai dai mambobi biyu na Civilian JTF da wani mai gadi sun rasa rayukansu a fafatawar.
