Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa dakarun soji sun fice daga Yelwata ne bayan samun rahoton ƙarya daga wani ƙauyen makwabta, lamarin da ya bai wa ‘yan ta’adda damar kai mummunan hari.
Ya ce rahoton ya yaudari dakarun zuwa wani wuri dabam da zargin hari, amma da zarar sun bar Yelwata, sai maharan suka kai farmaki suka hallaka fararen hula da dama.
Janar Musa ya zargi wasu mazauna yankin da taimaka wa ‘yan ta’adda da bayanai kan inda sojoji ke tsayawa da kayan aikinsu, har ma da kai musu abinci da mata.
Ya ce sai an inganta shugabanci da jin daɗin al’umma kafin a samu cikakken haɗin kai da goyon bayan jama’a wajen yaki da ‘yan ta’adda.
