Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiDalilin da ya sa ake fasa-kwaurin man fetur duk da cire tallafin...

Dalilin da ya sa ake fasa-kwaurin man fetur duk da cire tallafin man da aka yi – Hukumar Kwastam

Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya Adewale Adeniyi, ya ce al’adar fasa kwaurin mai na ci gaba da yaɗuwa ne saboda bambancin farashin man fetur tsakanin Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita.

Da yake jawabi yayin taron bitar watanni uku na farkon 2025 da hukumar ta gudanar a Abuja ranar Talata, Adeniyi ya lura cewa duk da cire tallafin man fetur, hakan bai hana masu fasa-kwauri fitar da mai daga Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Shugaban na Kwastam ya jaddada cewa, gagarumin gibin farashin na ci gaba da kara yawaitar fasa-kwauri.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata