Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya ce gurinsa na bunkasa masana’antu a Najeriya ne ya sa ba ya da gidaje a kasashen waje.
Dangote ya bayyana cewa samun gidaje a Landan ko Amurka zai dauke masa hankali wajen samar ma Najeriya masana’antu.
Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a matatar man Dangote da ke yankin Ibeju-Lekki a jihar Legas.
Ya ce, “Dalilin da ya sa ba ni da gida a Landan ko Amurka shi ne kawai don ina so in mayar da hankali kan bunkasa masana’antu a Najeriya.

