Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya shiga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne domin yana da tabbacin za ta samar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wani bikin godiya a cocin St. James Anglican dake Asokoro, Abuja, bisa kammala wasu ayyuka da kaddamar da su.
A cewar Wike, gwamnatin Tinubu ta cimma gagarumin nasara cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ya ce Shugaban kasa yana da jajircewa wajen tafiyar da mulki tare da bai wa ministoci umarnin ganin an kawo ci gaba a kasa.
Ministan ya kuma yi kira ga cocin da kada ta saurari tsofaffin shugabanni da ‘yan siyasa masu son kai, yana mai cewa hadakar jam’iyyun hamayya karkashin tutar ADC na kokarin rusa kasar.
Jaridar The Nation ta ambato Wike na cewa hadakar ba’a gina ta a doron gaskiya ko kwararan manufofi ba, yana tambayar dalilin kafa ta da kuma abin da suka sa a gaba.
