Shugaban riko na jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar da su zauna cikin hadin kai bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
A yayin taron kwamitin zartaswa na kasa (NWC) da aka gudanar a Abuja ranar Litinin karo na farko tun bayan barin Ganduje mukamin shugabancin APC, Dalori ya gargadi mambobi da su guji kalamai da abubuwan da ka iya jefa jam’iyyar cikin rikici.
Jaridar Punch ta ambato Dalori ya kara da cewa zai gabatar da tsarin aiki domin jagorantar jam’iyyar a wannan lokacin, wanda zai shafi ladabtarwa, sulhu, yada bayanai, hada kan mambobi da tuntubar masu ruwa da tsaki.
