Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiDan marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu

Dan marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu

Abdulmannan Abubakar Giro Argungu ya rasu a wannan Asabar, kusan shekaru biyu bayan rasuwar mahaifinsa.

Matashin shi ne da na tara cikin‚ ‘ya’yan babban malamin addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu.

A wata hira da DCL Hausa ta yi da shi a 2024, matashin, ya ce ya koyi gudun duniya da riko da addini daga mahaifinsa wanda ya rasu a watan Satumba na 2023

Abdulmannan ne dai ke jagoran masu kula da shafin sada zumunta na marigayi Sheikh Abubakar Giro.

Matashin da ya kammala karatun digirinsa jami’ar Maryam Abacha ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya. An jima da karfe 2:30pm ake sa ran yi masa jana‘iza a garin Argungu, jihar Kebbi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata