Rahotanni sun ce kocin kungiyar, Jorge Jesus, ya tabbatar da cewa Ronaldo zai yi tafiya zuwa Spain domin samun kulawa ta musamman daga wani kwararren likita da ke kula da lafiyarsa.
Fabrizio Romano ya rawaito cewa an yanke shawarar kai shi Spain ne domin a ba shi kulawa ta musamman da za ta taimaka wajen warkar da raunin cikin gaggawa.
Sai dai har yanzu ba a bayyana irin raunin da Ronaldo ya samu ba, amma ana sa ran karin bayani zai fito daga kungiyar Al-Nassr FC nan gaba.
