Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiDangote ya rage farashin man fetur da Naira 30 kan kowace lita...

Dangote ya rage farashin man fetur da Naira 30 kan kowace lita a tasoshin daukar mai

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga Naira 850 zuwa Naira 820 kan lita a matakin depo.

Tuni wannan farashin ya fara aiki tun ranar Talata, 12 ga Agusta, 2025.

A wata sanarwa da Anthony Chiejina, jami’in yada labarai na kamfanin, ya fitar, ya bayyana cewa matakin na daga cikin jajircewar kamfanin wajen ci gaban kasa tare da tabbatar da isar da man fetur ba tare da tangarda ba.

Haka kuma, kamfanin zai fara tura motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) domin rarraba mai a fadin Najeriya daga ranar 15 ga Agusta, 2025.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata