Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaDan takarar mataimakin gwamnan Kaduna a zaben 2023 ya fice daga jam'iyyar...

Dan takarar mataimakin gwamnan Kaduna a zaben 2023 ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa ADC

John Ayuba, wanda ya tsaya takarar mataimakin gwamnan Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar ADC.

Rahoton jaridar Punch ya Ambato wasikar da Ayuba ya tabbatar da sauya shekar tasa ne, da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na unguwar Ungwan Gaiya, da ke karamar hukumar Zangon Kataf.
Ya bayyana rashin jagoranci da cin amanar jam’iyya daga manyan jiga-jigai na ƙasa a matsayin dalilin ficewarsa.

Sa’annan ya kuma zargi wasu jiga-jigan PDP da cin amanar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben da ya gabata da kuma gaza ɗaukar matakin gyara tafiyar har zuwa yanzu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata