Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiDarajar Naira ta fadi, inda ake sayar da duk Dalar Amurka daya...

Darajar Naira ta fadi, inda ake sayar da duk Dalar Amurka daya kan Naira 1,608

Faduwar darajar Naira ta ci gaba a Larabar makon nan yayin da Nairar ta kara raunana a kasuwar canji, inda aka tashi a daren Larabar da farashin N1608 kan kowace Dala daya.

A ranar Talata, Naira ta fadi da N1 inda aka rufe kasuwar canji da farashin N1606.64 kan Dala daya a kasuwar musayar kudade ta Nijeriya.

A cewar bayanan da babban bankin CBN ya fitar, Naira ta fadi da kusan N3 a kan kowace Dala daya a ranar Litinin, inda aka rufe kasuwar canjin da farashin N1605.62 daga N1602.18 a ranar Juma’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata