Sunday, April 5, 2026
HomeNishadiDavido ya ce ya zuba dala milyan 3.7 fiye da Naira bilyan...

Davido ya ce ya zuba dala milyan 3.7 fiye da Naira bilyan biyar a bikin aurensa da Chioma

Shahararren mawakin Afrobeats, David Adeleke (Davido), ya bayyana cewa ya kashe dala miliyan 3.7 kwatankwacin Naira biliyan biyar, da miliyan dari shida da sittin da bakwai, a shirye-shiryen bikin aure na fari da matarsa, Chioma, da za a yi a Miami wannan karshen mako.

Bikin zai kasance na uku ga ma’auratan, bayan na kotu a Maris 2023 da na gargajiya a Legas a Yuni 2024.

Taron zai sami halartar fitattun ’yan Najeriya, ciki har da Gwamnan Osun, Ademola Adeleke.

Davido da Chioma sun fara haduwa sama da shekara 10 da ta gabata, kuma sun fuskanci kalubale, ciki har da rasuwar dansu Ifeanyi a 2022, kafin su haifi tagwaye a 2023 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya tattaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata