Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaDimukuradiyyar Nijeriya na cikin barazana a mulkin Tinubu - Atiku Abubakar

Dimukuradiyyar Nijeriya na cikin barazana a mulkin Tinubu – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan karancin fitowar masu kada kuri’a a zaben da aka gudanar ranar Asabar a Abuja.

Cikin wani sako da hadiminsa Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X, ya ce hakan na nuni da irin bazaranar da dimukuradiyya a Nijeriya ke fuskanta karkashin gwamnatin shugaba Tinubu.

Ya yi zargin cewa rashin fitowar masu zaɓe, na da alaka da yanayin tsoratarwa da kuma tauye ‘yancin yan adawa da ya ce ana yi a kasar, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata