Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiDino Melaye ya soki gwamnatin Tinubu kan yawan ciyo bashi

Dino Melaye ya soki gwamnatin Tinubu kan yawan ciyo bashi

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya soki gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa tana ciyo bashi da kuma kashe kuɗaɗe cikin rashin tsari.

A cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise, Melaye ya yi gargadin cewa idan gwamnatin ba ta daina ciyo irin wadannan basussukan ba, har kananan kamfanoni ma ba za su bari ba.

Ya ce akwai rashin hujja a cikin bukatar gwamnatin na neman bashin dala biliyan 1.7 daga babban bankin duniya, baya ga amincewar majalisar dattawa da kusan dala biliyan 21 na bashi daga ƙasashen ƙetare.

A cikin hirarsa ya ce gwamnatin tana yawan karbo bashin ne ba tare da aiwatar da wasu muhimman ayyuka ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata