Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaIyabo Obasanjo ta shiga jam'iyyar APC

Iyabo Obasanjo ta shiga jam’iyyar APC

‘Yar tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo, Iyabo Obasanjo, ta koma siyasa bayan kusan shekaru 15, inda ta shiga jam’iyyar APC a Jihar Ogun gabanin zaɓen 2027.

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa tsohuwar sanata da ta wakilci Ogun ta tsakiya a 2007 – 2011, ta kammala rajistar jam’iyyar APC a Ibogun, Ward 11, ƙaramar hukumar Ifo, yayin atisayen rijistar jam’iyyar da ake yi ta yanar gizo.

Iyabo, wacce kwararriyar masaniyar cututtuka (epidemiologist) ce kuma tsohuwar Kwamishiniyar Lafiya ta Ogun, ta sha kaye a yunƙurin sake komawa majalisa a 2011, kafin ta koma Amurka inda ta kai matsayin farfesa a harkar ilimi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata