Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiDokar ta baci a Ribas ta sa Fubara ya yi sanyi -...

Dokar ta baci a Ribas ta sa Fubara ya yi sanyi – Dattawan jihar

Daidai lokacin da wa’adin dokar ta baci ke shirin karewa a Ribas, dattawan jihar sun nuna shakku kan yiwuwar dawowar Siminalayi Fubara cikin karsashi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa har zuwa wannan lokaci da ya rage ‘yan kwanaki kantoman jihar Ibok-Ete Ekwe Ibas mai ritaya ya yi bankwana da gidan gwamnati, ba a samu wata sanarwa ko tattaunawa daga wajen Fubara ba.

Sai dai wani mataimakinsa wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa jaridar cewa Fubara zai sauka a jihar cikin ranakun karshen mako, domin ci gaba da jagoranci a matsayin gwamna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata