Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa dokar zaman gida da kungiyoyin IPOB ke tilastawa a kudu maso gabas na raguwa sosai.
Da yake jawabi a taron APC a Abuja, Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji manyan kalubalen tsaro guda biyar, ciki har da Boko Haram a Arewa Maso Gabas da ‘yan awaren IPOB a Kudu Maso Gabas.
Ya ce hadin gwiwar hukumomin tsaro ta taimaka wajen dakile hare-hare, satar mutane da barnar da mahara ke yi a sassan Nijeriya.
