Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiDSS ta bukaci kamfanin X ya sauke shafin Sowore

DSS ta bukaci kamfanin X ya sauke shafin Sowore

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bukaci kamfanin X, wanda aka fi sani da Twitter a da, da ya rufe shafin Omoyele Sowore, mai wallafa jarida kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa.

A cikin wata takardar ƙorafi, hukumar ta bai wa dandalin sada zumuntan sa’o’i 24 kacal don yin hakan.

A wasikar da wani B. Bamigboye ya sanya wa hannu a madadin Darakta Janar na DSS, hukumar ta yi barazanar ɗaukar matakai masu tsauri,  idan har dandalin bai amsa bukatarta ba.

Hukumar ta ce wani rubutu da Sowore ya wallafa kan Shugaba Bola Tinubu a ranar 25 ga Agusta, 2025, na iya tada tarzoma da kuma barazana ga tsaron ƙasa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata