Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiDuk wata hadaka da ke da nufin kayar da Shugaba Tinubu a...

Duk wata hadaka da ke da nufin kayar da Shugaba Tinubu a 2027 ba za ta yi nasara ba – Jigon APC

Jigo a jam’iyyar APC jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce hadakar da jam’iyyun adawa ke ci gaba da yi na kalubalantar shugaban kasa Bola Tinubu, ba za ta yi nasara ba.

Mista Oyintiloye, mamba a rusasshiyar majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a Osogbo.

Ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Peter Obi, da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wadanda su ne gaba-gaba wajen hadakar, da kada su wahalda kansu da dukiyarsu a kan aikin da ba zai yiyu ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata