Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiEFCC na binciken wasu mutane kan kudin jabu na Dala $899,800 a...

EFCC na binciken wasu mutane kan kudin jabu na Dala $899,800 a Kano

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nijeriya ta ce tana binciken wasu mutane biyu da ake zargi da tu’ammali da kudin jabu, inda ta ce an kama su da kudin Dala har $899,800.

Jami’an hukumar NDLEA ne dai suka kama Abubakar Hussaini da Sahabi Adamu a Wudil, kan titin zuwa Maiduguri jihar Borno kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na X.

Sanarwar ta ce mutanen biyu na tafiya ne a cikin wata mota kirar Golf 3 kan hanyar zuwa kauyen Kila da ke karamar hukumar Gwaram a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata