Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiEFCC ta cafke masu zamba a yanar gizo a samamen da ta...

EFCC ta cafke masu zamba a yanar gizo a samamen da ta kai Otal din Obasanjo da ke Abeokuta

Jami’an EFCC sun kai samame a Green Legacy Hotel da ke cikin Olusegun Obasanjo Presidential Library a Abeokuta, jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin masu zamba ne ta intanet.

Rahotanni sun ce an kama sama da motoci ma su tsada 20 da wasu kayayyaki a daren Lahadi yayin wani biki.

Gidan talabijin na Channels ya ambato shugaban harkokin kasuwanci na Otal doin, Vitalis Ortese, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayyana cikakkun bayanai ba.

Mai magana da yawun EFCC na Lagos, Ayo Oyewole, ya ce bai da cikakken bayani kan samamen amma zai bincika.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata