Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaEl-Rufai ya isa kotu kan neman beli a Kaduna

El-Rufai ya isa kotu kan neman beli a Kaduna

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna domin ci gaba da sauraron bukatar ba da belinsa.

Ya isa kotun da misalin karfe 9 na safe a ranar Laraba, a karkashin tsauraran matakan tsaro da jami’an ‘yan sanda da na DSS suka kafa.

Zaman kotun ya biyo bayan dage shari’ar da alkalin kotun, Mai shari’a Rilwan Aikawa ya yi a ranar Talata, sakamakon wasu sabbin matakan shari’a tsakanin bangaren wanda ake kara da na masu gabatar da kara.

Lauyoyin El-Rufai karkashin jagorancin Ubong Akpan sun fara gabatar da bukatar alkalin ya janye daga shari’ar bisa zargin son kai, amma daga baya suka janye wannan bukata, lamarin da ya janyo tsaiko a shari’ar.

Bangaren masu gabatar da kara ma sun gabatar da takardar martani suna adawa da bayar da beli, abin da ya bai wa bangaren wanda ake tuhuma lokaci kadan don mayar da martani, wanda hakan ya sa aka dage sauraron shari’ar zuwa ranar Laraba.

Ana zargin El-Rufai da aikata laifuka da suka hada da zamba, wawashe kudade da kuma mallakar kudaden jama’a ba bisa ka’ida ba, inda Hukumar ICPC ta shigar da karar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata