Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya kasancewa a bayan yunƙurin dan Majalisar Dokokin Amurka, Riley Moore, na sanya tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jerin sunayen da za a kakaba wa takunkumi kan zargin take ‘yancin addini.
Da yake magana a shirin Prime Time na Arise TV, El-Rufai ya ce saka sunan Kwankwaso cikin kudirin dokar da Moore da Chris Smith suka gabatar ba adalci ba ne, yana mai danganta lamarin da kin komawar Kwankwaso jam’iyyar APC da kuma jita-jitar komawarsa ADC.
Kudirin dokar ya tanadi kakaba takunkumi ciki har da hana biza da daskarar da kadarori ga wasu da ake zargi da hannu a take ‘yancin addini a Nijeriya, inda aka ambaci Kwankwaso da wasu kungiyoyi makiyaya.
Sai dai El-Rufai ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi taka-tsantsan, yana mai cewa matsalar tsaro a ƙasa ta shafi kowa ba tare da la’akari da addini ba, tare da sukar tsarin tsaro da ya ce ya gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
