Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiFarashin kayan abinci ya sauka a fadin Nijeriya – Ministan Noma

Farashin kayan abinci ya sauka a fadin Nijeriya – Ministan Noma

Ministan Noma a Nijeriya Abubakar Kyari, ya bayyana cewa an samu saukar farashin kayan abinci a fadin Nijeriya.

Ministan ya yi wannan bayani ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE ranar Juma’a.

A cewarsa, matakan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka wajen tabbatar da harkokin noma sun fara tasiri, inda ya ce gwamnatin tarayya ta yi amfani da dabaru wajen shigo da wasu kayayyakin abinci domin magance matsalolin da suka dade suna damun harkokin noma a Nijeriya.

Ya bayyana cewa akwai gibin samar da kayayyakin abinci da ake fuskanta, inda ya ce a shinkafar da ake nomawa a kasar, akwai gibin kashi 15% tsakanin abin da ake bukata da kuma abin da ake samarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata