Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiFarashin shinkafa ya karye a kasuwannin Legas

Farashin shinkafa ya karye a kasuwannin Legas

Farashin shinkafa ya sauka sosai a kasuwanni da dama na birnin Legas, sakamakon yawaitar shigowar shinkafa ta kan iyakoki.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito, buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yanzu yana tsakanin ₦55,000 zuwa ₦70,000 bisa, ya danganta da nau’in da mutum ke so.

Wasu ’yan kasuwa da masu sayen shinkafa da suka yi magana da NAN a Legas sun ce shinkafa ta cikin gida da ta waje sun sauka sosai idan aka kwatanta da farkon shekara.

A kasuwannin Oyingbo, Arena (Oshodi), Festac Town, da Mile 12, buhun shinkafa ta cikin gida da ake sayarwa ₦85,000 a watan Janairu yanzu tana tsakanin ₦60,000 zuwa ₦70,000, yayin da ta waje da ta kai ₦95,000 a baya yanzu ke tsakanin ₦65,000 zuwa ₦75,000.

Wata ’yar kasuwa a Arena Market, Hajiya Precious Okoro, ta ce faduwar farashin ta jefa ’yan kasuwa da dama cikin asara saboda rashin dawowar jarin da suka zuba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata