Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiDole ne fasinjojin jiragen saman Nijeriya su rufe wayoyinsu a lokacin tashi...

Dole ne fasinjojin jiragen saman Nijeriya su rufe wayoyinsu a lokacin tashi da sauka

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya NCAA ta bayyana cewa duk fasinjoji a Najeriya dole su kashe wayoyinsu gaba ɗaya a yayin tashin jirgi da sauka.

Shugaban hukumar ta NCAA, Chris Najomo, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce daga yanzu babu sauran amfani da “flight mode” a yayin tashin jirgi.

Rahoton jaridar Daily Nigerian ya ce umarnin ya biyo bayan takaddama tsakanin wata fasinja, Comfort Emmanson, da ma’aikaciyar jirgin Ibom Air, wacce ta jawo cece-kuce a filin jirgin saman Legas a kwanan nan.

Najomo ya ce wannan mataki zai kawo ƙarshen sabanin dokokin da kamfanonin jiragen sama ke bayarwa, tare da tabbatar da tsaro da daidaito a harkar tashi da saukar jiragen a kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata