Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaFilayen jiragen saman Nigeriya na tafka asara saboda karancin masu saka hannun...

Filayen jiragen saman Nigeriya na tafka asara saboda karancin masu saka hannun jari – Festus Keyamo

Ministan sufurin jiragen sama da ci gaban sararin samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana gudanar da filayen jirgin sama na Najeriya cikin asara, inda ya ce ba za ta iya ci gaba da kula da su ba tare da hadin gwiwa da masu zuba jari masu zaman kansu ba.

Keyamo ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da kamfanin jirgin sama na jihar Enugu mai suna Enugu Air, a kudu maso Gabashin Nijeriya.

Ministan ya bayyana cewa filin jirgin saman Enugu ba za a sayar da shi ba, amma za a mika shi hannun masu zuba jari ta hanyar tsarin haya da amfani (concession).

Gidan talabijin na Channels ya Ambato Keyamo na cewa wannan mataki zai bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata