Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiFilin jirgin saman Bola Tinubu dake Minna zai zama madadin filin jirgin saman Abuja...

Filin jirgin saman Bola Tinubu dake Minna zai zama madadin filin jirgin saman Abuja duk lokacin da aka samu matsala – Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin tarayya ta ayyana filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu, dake Minna jihar Neja a matsayin madadin filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe na Abuja.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ne ya bayyana haka a wajen ƙaddamar da tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu, inda jirgin sama na Overland Airways ya fara tashi.

Keyamo ya ce filin jirgin yana da tsari da yanayin da ya dace da kowane filin jirgin sama na kasa da kasa a fadin duniya, kuma za a rika amfani da shi a duk lokacin da aka samu cunkoson jirage ko wata matsala a filin jirgin sama na Abuja.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata