Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya sauke dukkanin kwamashinoni da sauran makarraban gwamnatinsa.
Gwamnan ya sanar da matakin ne, a yayin jawabinsa na bikin ranar ‘yancin kan Nijeriya karo na 65, inda ya jingina matakin da hukuncin kotun koli na baya -bayan nan.
Wanda ta tabbatar da Martin Amaewhule a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Rivers na doka, lamarin da ya rusa sahihancin matakan da Victor Oko-Jumbo ya dauka lokacin da yake rike da kujerar shugabancin majalisar.
Saboda haka, an kiyasta cewa, kasa da kwamishinoni goma ne za su ci gaba da rike mukamansu, kafin a sake kafa sabuwar majalisar zartarwa a jihar.
