Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiFulani ake sacewa fiye da Yarbawa a jihar Kwara – Shugaban karamar...

Fulani ake sacewa fiye da Yarbawa a jihar Kwara – Shugaban karamar hukuma

Shugaban karamar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara, Hajji AbdulRasheed Yusuf, ya bayyana cewa sama da kashi 98 cikin 100 na waɗanda ake sacewa a Kudancin jihar Fulani ne, ba Yarbawa ba kamar yadda ake yawan yadawa.

Yusuf ya yi wannan bayani ne a yayin shirin “Newskeg” na kungiyar ɗaraktocin ƙungiyar ƙwararrun ƴan jarida ta Najeriya (NUJ) da aka gudanar a sakatariyar hukumar a Ilorin.

Ya ce akwai damuwa sosai yadda hukumomin tsaro sukan tabbatar wa da hukumar cewa mafi yawan waɗanda ake yin garkuwa da su a yankin Fulani ne.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi ya kuma bayyana cewa masaniyar sirri ta nuna cewa masu ba barayin bayanai na fakewa ne a kasuwannin shanu na jihar.

Ya ƙara da cewa, a baya shugabannin kananan hukumomi bakwai na yankin Kwara ta Kudu sun yanke shawarar rufe dukkan kasuwannin shanu, amma daga baya suka janye wannan mataki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata