Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiFursunoni 16 sun tsere daga kurkukun Keffi da ke jihar Nasarawa a...

Fursunoni 16 sun tsere daga kurkukun Keffi da ke jihar Nasarawa a Nijeriya

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya (NCoS) ta ce fursunoni 16 suka tsere daga gidan yari na Medium Security da ke Keffi, jihar Nasarawa, da saiyar ranar Talata.

Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Umar, ya ce wasu fursunoni sun karya tsaron wurin, suka kai wa jami’an da ke bakin aiki hari, lamarin da ya haifar da tserewar su.

A kokarin shawo kan matsalar, jami’ai biyar sun ji raunuka daban-daban, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali suna karbar kulawar gaggawa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tattaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata