DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiFursunoni 68 ne suka samu nasara a jarabawar NECO ta 2025 a...

Fursunoni 68 ne suka samu nasara a jarabawar NECO ta 2025 a jihar Kano

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa fursunoni 68 sun samu nasara a jarabawar NECO ta shekarar 2025.

Mai magana da yawun hukumar a jihar, CSC Musbahu Lawan, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano a ranar Litinin.

Ya ce wannan nasara ta samu ne sakamakon ingantaccen tsarin koyarwa na cibiyar gidajen gyaran hali da kuma cikakken tallafin gwamnatin Jihar Kano.

A cewarsa, shirin ya nuna yadda ake aiwatar da dokar Correctional Service Act ta shekarar 2019, wacce ta bai wa fursunoni damar koyon karatu da sana’o’i a gidajen yari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata