Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGaggawa ba za ta sa mu kauce wa bin doka ba -...

Gaggawa ba za ta sa mu kauce wa bin doka ba – Martanin INEC ga hadakar jam’iyun da ke son yin rajista

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a Nijeriya ta shaida wa gamayyar kungiyoyin siyasa masu neman rajistar sabuwar jam’iyya gabanin zabukan shekarar 2027, cewa duk wani matsin lambarsu ba zai sa hukumar ta ki bin dokokin tsarin mulki da na kasa.

Hukumar zaben ta nuna shakku kan bin dokoki wajen gabatar da jam’iyyun, inda ta yi gargadin cewa ba ayyana jam’iyya ne zai sa ta samu rajista ba, akwai tsauraran ka’idoji da kundin tsarin mulki ya tanada.

INEC ta kuma musanta rahotannin da ke yawo a yanar gizo cewa, ta yi wa sabbin jam’iyyun siyasa biyu rajista wato “Independent Democrats” da “People Democratic Movement.”

A baya-bayan nan dai wasu ‘yan adawa da dama sun zargi hukumar zaben da kin yiwa sabbin jam’iyyun siyasa rajista, lamarin da ya haifar da fargaba kan basu damar shigar da zabe.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata