DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiGamayyar kungiyoyin jam'iyyar APC reshen Arewa ta tsakiyar Nijeriya sun yi kira...

Gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC reshen Arewa ta tsakiyar Nijeriya sun yi kira ga shugaba Tinubu da majalisun kasar cewa kar su amince da kirkirar ‘yan sandan jihohi

Gamayyar kungiyoyin APC na Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, da Majalisar dokoki ta kasa da su ƙi amincewa da kiran kafa ’yan sandan jihohi a Nijeriya.

Ƙungiyar ta yi wannan roƙon ne a martanin da ta mayar kan furucin Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, wanda ya yi kira a makon da ya gabata cewa lokaci ya yi da za a kafa ’yan sandan jihohi domin inganta tsaro musamman a jihar Filato da sauran sassan Nijeriya.

Sai dai a wata sanarwa da Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Saleh Zazzaga, ya fitar a Abuja, ƙungiyar ya yi gargaɗi cewa kafa ’yan sandan jihohi zai zama hanya ta yin danniya da zaluntar daidaikun mutane da kuma ’yan adawa a jihohi.

Sanarwar ta kuma yi hasashen cewa kafa ’yan sandan jihohi zai iya zama barazana ga tsarin dimukraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata