Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGamayyar kungiyoyin matasan jihar Rivers sun bukaci shugaba Tinubu ya mayar da...

Gamayyar kungiyoyin matasan jihar Rivers sun bukaci shugaba Tinubu ya mayar da Fubara da sauran ‘yan majalisar dokokin jihar kujerunsu

Gamayyar kungiyoyin matasa a jihar Rivers sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dawo da mulkin dimokaradiyya a jihar tare da mayar da gwamna Siminalayi Fubara gabanin bikin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yuni.

Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Imeabe Oscar, shugaban kungiyar matasan Kudu-maso-Kudu na kasa wanda ya zama shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin matasan jihar Ribas ya aike wa manema labarai.

Kungiyoyin matasan cikin rahoton da jaridar Punch ta wallafa a ranar Talata, sun bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa Fubara barazana ce kai tsaye ga tsarin mulkin kasar da kuma barazana ga tushen dimokuradiyya a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata