Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGarken giwaye a jihar Ogun sun yi ajalin wani manoni a yankin...

Garken giwaye a jihar Ogun sun yi ajalin wani manoni a yankin karamar hukumar Ijebu

Wani manomi mai shekaru 49 mai suna Musa Yahaya Kala ya rasa ransa bayan da giwaye suka kai masa hari a kauyen Itasin da ke karamar hukumar Ijebu East, Jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da hantsi a ranar Litinin, inda manomin ke tare da dansa lokacin da giwayen suka kai harin.

Rahoton Jaridar Daily Trust ya ce al’ummar yankin sun bayyana fargaba da fusata kan yadda ake ta fuskantar rikici tsakanin mutane da dabbobin jeji a yankin sau da dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata