Monday, April 6, 2026
HomeKetareGhana ta fara karbar 'yan kasashen yammacin Afirka da Amurka ta koro

Ghana ta fara karbar ‘yan kasashen yammacin Afirka da Amurka ta koro

Shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ya tabbatar da cewa ƙasarsa ta fara karɓar wasu ‘yan ƙasashen Yammacin Afirka da Amurka ta koro, ciki har da ‘yan Nijeriya.

Mahama ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce wannan mataki ya biyo bayan wata yarjejeniya ta diflomasiyya da aka kulla.

Shugaban ya ƙara da cewa matakin ya shafi ƙasashen yammacin Afirka daban-daban, kuma Ghana za ta yi aiki tare da hukumomin ƙasashen da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an dawo da waɗanda aka koro cikin mutunci da tsari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata