Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan, yana cikin koshin lafiya kuma ya bar Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin kasar, in ji sanarwar gwamnatin Nijeriya a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje Nijeriya, Kimiebi Ebienfa ne ya tabbatar da hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce Jonathan ya tashi tare da tawagarsa ciki har da Mohamed Chambas.
Ma’aikatar ta ce Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban kwamitin kula da zabe na zauren dattawan yammacin Afirka, domin sa ido kan zaben shugaban kasa da na majalisa da aka gudanar a ranar Lahadi, kafin sojoji su sanar da cewa sun karɓe mulki.
Bayan rufe iyakokin kasar, a ranar Alhamis hukumomin sojin suka sanar da bude iyakokin, inda Janar Lansana Mansali, babban mai kula da rundunar
sojin Guinea-Bissau, ya tabbatar da daukar matakin.
