Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGuguwar iska ta lalata gidaje fiye da 1,400 tare da yin ajalin...

Guguwar iska ta lalata gidaje fiye da 1,400 tare da yin ajalin mutum biyar a Jihar Sokoto.

Guguwar iska mai karfi ta yi ajalin mutane biyar tare da lalata gidaje sama da 1,400 a kananan hukumomin Gwadabawa da Kware da ke jihar Sokoto, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta tabbatar.

Hukumar ta bayyana cewa guguwar ta bar mutane da dama da raunuka, kana ta shafi muhimman gine-gine kamar makarantu, ofisoshin gwamnati da wasu wuraren jama’a.

SEMA ta ce tuni ta aika jami’anta domin tantance barnar da aka yi da tattara cikakkun bayanai, domin ɗaukar matakan da suka dace wajen tallafa wa al’ummar da lamarin ya shafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata