Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin binciken belin kasurgumin dilan...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin binciken belin kasurgumin dilan kwayoyi da ake zargin kwamishinansa ya yi

A yayin kaddamar da kwamitin binciken mai ƙarfi wanda zai gudanar da cikakken bincike kan lamarin, gwamnan ya bayar da wa’adin mako guda kacal domin gano gaskiyar al’amari tare da bayar da rahoto.

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya wakilci Gwamnan wajen kaddamar da kwamitin, inda ya bayyana cewa wannan mataki na cikin kudirin gwamnatin Kano na yaki da miyagun ƙwayoyi da kuma tabbatar shugabanci na gari.

Sakataren Gwamnati ya ce an zaɓi mambobin kwamitin ne bisa cancanta, ƙwarewa, jajircewa da ƙwarin guiwar cika alƙawarin da aka ɗora musu.

A madadin sauran mambobin, shugaban kwamitin, Barrister Aminu Hussaini, ya gode wa Gwamnatin Kano bisa daukar matakin gaggawa, tare da alkawarin gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da kwarewa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata