Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhini kan harin ‘yan bindiga da ya auku a ƙaramar hukumar Bukkuyum, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
Kamar yadda sanarwar mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ta bayyana, harin ya faru ne da daddare a yankunan Bunkasau, Yar Galma (Zarumai Ward) da Dogon Daji (Adabka Ward), inda aka kai farmaki kan fararen hula ba tare da wani dalili ba.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin tausayi, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata.
Ya kuma umarci a tura wata tawaga ta musamman karkashin jagorancin mataimakin gwamnan domin kai ziyara, bayar da tallafi ga iyalai da kuma tabbatar da samun kulawar lafiya ga waɗanda suka ji rauni.
