Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaGwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya karyata jita-jitar komawa APC

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya karyata jita-jitar komawa APC

Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya karyata rade-radin cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Jaridar the Nation ta ruwaito Diri ya ce wannan rade-radin ya samo asali ne daga maganganun Ministan Ayyuka, David Umahi.

Wanda ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Sampou, yayin da ya karɓi baƙuncin dan majalisa mai wakiltar mazabar kudancin Ijaw, Rodney Ambaiowei, da wasu jiga-jigan siyasa.

Gwamnan ya ce bai damu da jita-jitar ba kuma hakan ba zai dagula masa lissafi ba, inda ya ce halartar taron kaddamar da wani ɓangare na titin ruwan teku na Lagos-Calabar ne ya janyo zargin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata