Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamna Zulum na jihar Borno ya sallami wasu kwamishinoninsa biyu daga mukamansu

Gwamna Zulum na jihar Borno ya sallami wasu kwamishinoninsa biyu daga mukamansu

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sauke kwamishinansa biyu daga muƙamansu.

Mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Kwamishinonin da abin ya shafa su ne na Ma’aikatar Muhalli, Injiniya Emat Kois, da kuma Kwamishinan Hulɗa da Gwamnatoci da Harkokin Musamman, Honarabul Tukur Ibrahim.

Hakama gwamnan ya sanar da nadin Injiniya Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan a matsayin sabbin kwamishinonin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata