Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya rattaba hannu a wasu dokoki guda biyu da suka haramta sare bishiyoyi da kuma ware rana daya a cikin kowane wata a matsayin ranar tsabtace muhalli a fadin jihar.
Zulum ya sanya ma dokokin hannu ne a Maiduguri da ke da nufin magance matsalolin gurbacewar muhalli da kuma inganta lafiyar al’umma.
Bayan haka, Gwamnan ya kara da cewa, duk wanda ya karya dokar za a ci shi tarar kudi Naira 250,000 ko kuma zama gidan gyaran hali na shekara 3 ga wanda karon farkonsa na karya dokar. Wanda kuma ba shi ne na farko bai zai biya tarar Naira 500,000 ko kuma shekaru 5 a gidan gyaran hali.
Bugu da kari, Zulum ya ware ranar Asabar ta farkon kowane wata a matsayin ranar tsabtace muhalli domin inganta lafiya da kuma kariya daga cututtuka a fadin jihar. Saba ma dokar ita ma na iya sa a ci tarar Naira 100,000 ko kuma zama gidan gyaran hali na shekaru 2.
